Game da dangantaka tsakanin kasashen biyu, Hu Jintao ya jaddada cewa, kasashen biyu na da bunkatun samun moriyar juna. Kamata ya yi, su kawar da duk wani shinge a tsakaninsu tare da kara bunkasa dangantakar dake tsakaninsu ta la'akari da moriyar jama'ar kasashen biyu da zaman lafiya duniya. Dadin dadawa, Hu ya ce, ko shakka babu, akwai wasu batutuwa masu daukar hankali a tsakaninsu, duk da hka, kamata ya yi, kasashen biyu su kara yin musayar ra'ayoyi da nuna amincewa da juna domin magance wadannan batutuwa yadda ya kamata ta yadda za a bunkasa dangantaka a tsakaninsu cikin lumana a dogon lokaci. Yayin da aka tabo batun amfani da dalar Amurka, Hu Jintao ya bayyana cewa, dala ta kasance muhimmiyar takardar kudi da ake amfani da ita a duniya, saboda haka, tsarin kudi na kasar Amurka yana yin babban tasiri kan kasuwannin kudi na duniya, ya kamata, ana ba da tabbaci ga tsarin yin amfani da dala. Ban da wanann kuma, game batun kudin Sin, Hu ya bayyana cewa, akwai abubuwa da dama da za a yi wajen mai da kudin Sin a matsayin kudin da za a iya yin amfani da shi a duniya ba tare da wani shinge ba.
Yayin da aka ambato batun halin da zirin Korea ke ciki, Hu Jintao ya bayyana cewa, a karkashin kokarin da kasar Sin da bangarori daban-daban suka yi, halin da ake ciki a zirin Korea ya sassauta. Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su yi amfani da zarafi mai kyau wajen farfado da shawarwari ta yadda za a kyautata halin da ake ciki a zirin.(Amina)