in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin CIBN zai kasance kafar watsa labarai dake taka muhimmiyar rawa a duniya
2011-01-17 15:39:30 cri
Ranar Talata 18 ga wata, gidan rediyon kasar Sin CRI zai kaddamar da tsarin kafofin watsa labarun kasa da kasa na kasar Sin da aka lakabawa suna CIBN a birnin Beijing. Kwanan baya, yayin da yake hira tare da wakilinmu, mataimakin babban edita na CRI Mista Ma Weigong ya ce, kafuwar tsarin CIBN ta zama wata alamar dake nuna cewa, an fara kokarin raya gidan rediyon CRI don ya zama wani hamshakin kamfanin watsa labarai a duniya. Haka kuma Mista Ma ya bayyana cewa, za'a nuna himma da kwazo wajen bunkasa tsarin CIBN, don ya zama wata kafar watsa labarai dake taka muhimmiyar rawa a duniya baki daya.

Mista Ma Weigong ya ce, tsarin CIBN zai kasance kafar watsa labarai ta farko a kasar Sin, wadda ke kunshe da hanyoyin sadarwa iri-iri, kuma ke watsa labarai cikin harsuna da dama. Ma ya ce:

"Tsarin kafofin watsa labarun kasa da kasa na kasar Sin CIBN, yana kunshe da abubuwa na kasar Sin tare da na kasa da kasa, haka kuma zai watsa labarai ta kafofin rediyo da talabijin duka. Ko da yake an kafa shi ne a nan kasar Sin, amma zai kasance wani tsarin dake kunshe da kafofin rediyo da TV a duniya, wadda ba'a taba ganin irinta ba a tarihi. Tsarin CIBN ya sha bamban da sauran kafofin watsa labarai da aka saba da su, inda zai watsa labarai ta hanyar amfani da sabbin fasahohi, kuma ta sabbin hanyoyin sadarwa."

A cikin 'yan shekarun nan, sakamakon gogayyar da ake yi tsakanin kafafen watsa labaran kasa da kasa, gami da ingantuwar matsayin kasar Sin a duniya, gidan rediyon CRI ya tsara burin zama wata kafar watsa labarai ta zamani, wadda ke watsa labarai ta hanyoyin sadarwa daban-daban kuma ke shafar fannoni da dama, a kokarin kara taka rawa wajen samun fahimtar juna da karfafa dankon zumunci tsakanin jama'ar kasar Sin da ta sauran sassan duniya baki daya. A halin yanzu, gidan rediyon CRI na tafiyar da ayyuka daga manyan fannoni biyar, ciki har da watsa shirye-shirye ta kafar rediyo, watsa labarai ta jarida, harkokin da suka shafi yanar gizo ko Intanet, wayoyin salula da talabijin da sauransu, kuma an kaddamar da tsarin CIBN ne a cikin irin wannan hali.

Yayin da yake zantawa kan nau'o'in ayyukan da tsarin CIBN zai tafiyar, Mista Ma Weigong ya nuna cewa:

"A matsayin wani tsarin kafofin watsa labaran kasa da kasa, a halin yanzu, CIBN na gudanar da ayyuka daga manyan fannoni uku. Na farko shi ne, dandalin watsa shirye-shirye ta kafar rediyo. Na biyu kuwa shi ne, dandalin tashar Intanet, ko 'CRI Online'. Na uku kuma na karshe shi ne, kafar talabijin dake amfani da yanar gizo ta Intanet.'"

Mista Ma Weigong ya kara da cewa, kafuwar tsarin CIBN na dacewa da bunkasuwar kafofin watsa labarai a duniya, inda ya ce:

"Ci gaban kafafen watsa labarai, tare kuma da bunkasuwar sana'ar watsa labarai, suna kawo babban kalubale ga kafofin watsa labarai irin na da a duniya, abun da ya sa kafofin watsa labarai da dama ke nuna hazaka wajen neman yin gyare-gyare, da lalubo sabuwar hanyar da za su bi wajen tafiyar da ayyukansu."(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China