in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman jami'an gwamnatin kasar Amurka sun dora muhimmanci sosai kan ziyarar da shugaban kasar Sin zai yi a kasar Amurka
2011-01-14 17:05:38 cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao zai ziyarci kasar Amurka daga ran 18 zuwa ran 21 ga wata, wannan ne karo na farko da zai ziyarci kasar Amurka bayan da Mr. Barack Obama ya hau kan karagar mulkin kasar. A shekarar bara, an samu wasu sabane-sabane a tsakanin kasashen Sin da Amurka, mutane da yawa na duniya suna dora muhimmanci sosai kan wane irin tasirin da wannan ziyara za ta kawo wa bunkasuwar huldar dake tsakanin kasashen biyu. A kwanan baya, wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Amurka sun yi jawabai, inda suka bayyana cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin Hu Jintao zai yi a kasar Amurka za ta samar da wani zarafin kawar da sabane-sabanen dake tsakanin bangarorin biyu da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu.

Kafin shugaba Hu Jintao ya ziyarci kasar Amurka, manyan jami'an kasashen biyu sun ziyarci juna domin aikin share fage. Shugaban taron hafsan-hafsoshin kasar Amurka Michael Mullen ya ce, ziyarar da ministan tsaron kasar Amurka Robert Gates ya yi a kwanan baya a kasar Sin ta karfafa huldar dake tsakanin sojojin kasashen biyu. Ya ce, "Muna begen ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi a kasar Amurka, ko da yake akwai kasancewar sabane-sabane a tsakaninmu, amma za mu fuskance su kuma kawar da su domin kara fahimtar juna."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China