Jon Hunsman ya nuna cewa, ganawa tsakanin shugabannin Sin da Amurka na da muhimmanci, domin wadannan kasashe biyu sun kasance manyan kasashen masu ci gaban tattalin arziki. Ya ce, a cikin shekara daya da 'yan watanni da suka wuce, shugaban kasar Amurka Barack Obama da shugaban kasar Sin Hu Jintao sun gana da juna har sau 7, an gudanar da shawarwari kan tattalin arziki da manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Yayin da ake kokarin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, an yi ta samun matsaloli, amma daidaiton da suka cimma ya zarce matsalolin da aka fuskanta, a nan gaba za a kara samun hadin gwiwa a tsakaninsu.
Kana ya furta cewa, kasashen biyu za su yi kokarin warware matsaloli daban daban na duniya, kamar batun nukiliya na kasar Iran, da halin da ake ciki a zirin Koriya, da sake kokartawa wajen daidaita tattalin arziki, da kuma batun sauye-sauyen yanayi.(Zainab)