Masanin da ake kira Lanpton yana ganin cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin zai kai Amurka tana da muhimmanci sosai, kuma wani babban burin da za a cimma wajen ziyara shi ne kara amincewa da juna tsakanin kasashen biyu, kana ma iya cewa haka ta cimma ruwa idan an cimma wannan buri.
Lanpton ya yi nuni da cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin zai kai kasar Amurka ta shaida cewa, kasashen biyu sun gano moriya bai daya tsakaninsu, kuma ya kamata a tabbatar da hulda a tsakaninsu yadda ya kamata. Har wa yau, ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu ta bangaren tattalin arziki da ciniki ma ka iya kara samar da amincewa da juna tsakaninsu.(Lubabatu)