Sanusi: madam Chen Fengying, shugabar sashen nazarin tattalin arzikin kasa da kasa a cibiyar nazarin huldar dake tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin tana ganin cewa, kara bukatu a kasuwar cikin gida za ta zama wata sabuwar damar raya tattalin arzikin kasar Sin. "Yadda za a sa kaimi ga jama'a su kashe kudi a kasuwa, ya kasance wani muhimmin matakin bunkasa tattalin arzikin kasarmu. Sannan, wani batu na daban shi ne zaman rayuwar jama'a. Dole ne a kebe karin kudade daga baitulmali kan ayyukan da suke da nasaba da zaman rayuwar jama'a."
Ibrahim: A cikin takardun da aka fitar a yayin wannan taro, an ce, za a daidaita tsarin bukatun da ake da su a kokarin da ake na inganta karfi da yanayi na sayayya. Sannan za a yi kokarin raya sana'o'in ba da hidima, kamar na ba da ilmi da kiwon lafiya da na samar da wuraren kwana da guraban aikin yi da kuma ba da tabbaci ga jama'a.
Sanusi: A hakika dai, a cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta samu ci gaba sosai a wadannan fannoni, amma har yanzu ba ta iya biyan bukatun jama'a ba. Musamman yanzu farashin gidajen kwana ya haura cikin sauri sosai, galibin jama'a ba su da isasshen kudin sayen wani gidan da suke bukata. Sakamakon haka, a gun wannan taro, an jaddada cewa, dole ne a hanzarta yin gyare-gyare kan manufofin samar wa jama'a gidaje masu rahusa da suke bukata. Kuma dole ne gwamnatoci a wurare daban daban su sauke wannan nauyin da aka dora musu. Kafin a yi wannan taro, hukumomin dake kula da aikin samar da gidajen kwana sun fitar da shirin samar da gidaje masu arha miliyan 10 a shekara mai kamawa. Game da wannan shiri, madam Chen Fengying tana mai cewa, wannan shiri zai taimaka wajen rage damuwar da jama'a ke fuskanta dangane da tsadar gidaje. "Lokacin da ake yin takara tsakanin kasuwa da manufofin gwamnati, abu mafi muhimmanci matuka a lokacin shi ne sa ido kan yadda kasuwa ke tafiyar da harkokin gidaje. Yanzu ana fuskantar wasu matsalolin da ba su dace ba, alal misali, matsalolin da 'yan kasuwa wadanda suke gina gidaje suka haifar, da matsalolin da wasu 'yan kasuwa suke yunkurin haifarwa na neman karin riba a duk wata damar da ta samu. A ganina, a cikin manufofin da aka tsara a yayin wannan taro, abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne yadda gwamnati ta amince da samar da gidaje masu saukin kudi ga jama'a. Wadannan gidaje masu arha za su taka muhimmiyar rawa wajen rage farashin gidaje a kasuwa."
Ibrahim: A cikin shekarar 2010, kasar Sin ta kuma fuskanci matsalar raguwar darajar kudinta. Alal misali, saurin hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 5.1 cikin kashi dari a watan Nuwamba bisa na watan Oktoba. Sabo da haka, a yayin wannan taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an sanya aikin rage saurin hauhawar farashin kayayyaki a cikin muhimman ayyukan da gwamnati za ta aiwatar a shekarar 2011.
Sanusi: Game da wannan manufa, madam Tan Yaling, shugabar cibiyar nazarin yin amfani da kudin musaya ta kasar Sin tana ganin cewa, lokacin da yawan kudin da ake zubawa a duk fadin duniya yake ta karuwa, kasar Sin tana ta fuskantar matsin lamba dangane da raguwar darajar kudinta. Sabo da haka, manufar kudi da za ta zauna da gindinta na nufin daidaita halin da ake ciki ta fuskar sha'anin kudi zai koma yadda ya kamata. "Babban bankin kasar Sin ya tabbatar da ma'anar 'manufar kudi da za ta zauna da gindinta', wato za a koma ga tsarin da aka saba a baya. Yanzu ana aiwatar da manufar kudi mai sassauci, ba a iya tinkarar hadarin da mai yiyuwa zai shafi farashin kayayyaki. Amma ba mu yi amfani da kalaman 'dawo' ko 'rage' ko 'sassauta' ba domin kokarin kwantar da hankalin jama'a. Wannan ne ya fi muhimmanci."
Ibrahim: Bugu da kari, madam Tan Yaling ta kara da cewa, "Bayan manufar kudi ta koma yadda aka saba yi, yawan takardun kudi da ake samarwa a kasuwa ya kan koma yadda ya kamata." (Sanusi Chen)