in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai wuya wajen magance rikicin siyasar kasar Cote D'ivoire
2011-01-06 13:36:23 cri

Ranar 4 ga wata, bayan da suka kawo karshen kokarin shiga-tsakanin da suka yi, shugabannin kasashen Afirka uku, ciki har da na Benin, Saliyo, da Cape Verde, tare da firaministan kasar Kenya Raila Odinga sun tashi daga birnin Abidjan na kasar Cote D'ivoire. Makasudin wannan ziyara ta wadannan wakilai na musamman hudu a Cote D'ivoire shi ne, domin bukatar Laurent Gbagbo da ya mika mulki ga Alassane Ouattara ta hanyar lumana, amma wannan kokarin dilomasiyya ya sake ci tura.

Manazarta suna ganin cewa, sakamakon halin kiki-kaka da ake ciki a kasar Cote D'ivoire, da batun tura sojoji zuwa kasar da kungiyar ECOWAS ke fuskanta, akwai wuya ainun a daidaita rikicin siyasar kasar Cote D'ivoire cikin wani dan kankanin lokaci. Kuma a halin yanzu, ana mayar da hankali sosai kan wadanne irin matakai ne kungiyar ECOWAS da kungiyar tarayyar Afirka za su dauka a nan gaba.

Ranar 3 ga wata, wakilai daga kasashen hudu sun yi shawarwari sau biyu tare da Laurent Gbagbo, tare kuma da ganawa da Alassane Ouattara. Daga baya, kakakin tawagar, wanda kuma shi ne shugaban kasar Saliyo Koroma ya ce, sun nuna kwazo wajen gudanar da shawarwari tsakaninsu. Sa'an nan a rana 4 ga wata da maraice, kungiyoyin ECOWAS da AU sun bayar da sanarwar dake cewa, Gbagbo ya yarda a kawo karshen rikici ta hanyar yin shawarwari ba tare da gindaya wani sharadi ba. Amma duk da haka, Gbagbo bai ce uffan ba a game da batun mika mulki.

Rahoto daga kafofin watsa labaran wurin ya ce, a yayin da suke ganawa da wakilan kasashen hudu, Gbagbo da Ouattara dukkansu sun bayyana cewa, za su tsaya kan matsayinsu, ba za su canja ba. A nasa bangaren, Gbagbo ya sake bada shawarar kafa wani kwamiti, a kokarin sake kirga kuri'un da aka jefa zagaye na biyu. Amma Ouattara ya ki amincewa da wannan shawara, inda ya ce, wannan wayo ne na Gbagbo, kuma ainihin nufinsa shi ne daukar lokaci, don haka Ouattara yayi kira ga Gbagbo da ya sauka daga kan mulki tun da wuri.

Ranar 24 ga watan Disamban shekara ta 2010, kungiyar ECOWAS ta kira wani taro musamman a Abuja, babban birnin kasar Najeriya, inda aka tattauna kan halin da ake ciki a kasar Cote D'ivoire, da bayar da wata sanarwa, inda aka yi kira ga Laurent Gbagbo da ya mika karagar mulki ga Alassane Ouattara ba tare da bata lokaci ba, in ba haka ba, za'a dauki duk wani matakin da ya wajaba, ciki har da karfin soji. Sa'an nan bayan kwanaki hudu, a madadin kungiyar ECOWAS, shugabannin kasashen Benin, Saliyo, da Cape Verde sun isa birnin Abidjan daya bayan daya, a kokarin neman Laurent Gbagbo da ya mika mulki cikin zaman lafiya.

Manazarta sun yi nuni da cewa, kokarin diflomasiyya da kungiyoyin ECOWAS da AU suka yi har sau biyu ya sha kaye, kuma da wuya a yi amfani da karfin soji wajen warware wannan matsala cikin wani dan lokaci kadan.

Wani jami'in Laurent Gbagbo ya ce, ba za'a dauki matakin soji ba. Haka kuma a ranar 4 ga wata, gwamnatin kasar Faransa ta nuna cewa, nauyin dake bisa sojojin kasar shi ne kare 'yan kasar Faransa, don haka ba za su dauki matakin soji ba a kasar Cote D'ivoire. Bugu da kari kuma, kasashe membobi da dama na kungiyar ECOWAS suna fuskantar matsaloli cikin gida, akwai wuya gare su wajen tura sojoji zuwa Cote D'ivoire. Kwanan baya, wani kakakin kungiyar ya fadi cewa, har yanzu ECOWAS ba ta yanke wata shawara ba, dangane da batun da ya shafi tura sojoji zuwa kasar Cote D'ivoire.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China