in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina aka kwana game da makomar kasar Cote D'ivoire?
2011-01-05 16:06:38 cri
Tun bayan ranar 28 ga watan Nuwanba na shekarar 2010, wato aka kammala babban zaben a kasar Cote D'ivoire, tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da jagoran jam'iyyar adawa Alassane Dramane Ouattara sun ci gaba da ja-in-ja game da sakamakon zabe a tsakaninsu, ko da yake, kasashen duniya sun amince da Ouattara ya cimma nasara a zaben, amma Gbagbo ya ki sauka daga mulkinsa. Kwanan baya, bayan da kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yi shawarwari har na zagaye biyu, an dan samu ci gaba game da wannan batu. A ranar 4 ga wata, bisa sanarwar da tawagar kungiyar ECOWAS da ta AU suka bayar cikin hadin gwiwa, an ce, Gbagbo ya amince yin shawarwari da kungiyar AU da ta ECOWAS ba tare da wasu sharudda ba, don warware rikicin kasar cikin ruwan sanyi.

A ranar 3 ga wata, tawagar kungiyar ECOWAS da ta AU ta yi tattaki zuwa kasar Cote D'ivoire, don tafiyar da shawarwari da bangarorin da abin ya shafa, kuma tawagar din ta yi shawarwari da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da jagoran jam'iyyyar hamayya Alassane Ouattara da wakilin musamman na sakatare janar na M.D.D da ke kasar Cote D'ivoire Young-Jin Choi. Haka kuma, a ranar 4 ga wata, wannan tawaga ta koma birnin Abuja wato inda hedkwatar ECOWAS take, don isar da sakamakon tawagar ga shugaban karba-karba na kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan, daga bisani kuma, an ba da hadaddiyar sanarwa. A cikin sanarwar, an ce, Gbagbo ya amince yin shawarwari don warware rikicin kasar Cote D'ivoire cikin lumana kuma ba tare da wasu sharudda ba, a sa'i daya kuma, ya amince da dage kawanyar da aka yi wa otel din da abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara ya kafa ofishinsa. Haka kuma, Ouattara ya ce, idan Gbagbo ya amince da sakamakon zabe da kwamitin zabe mai cin gashin kansa ya gabatar, kuma ya amince da ni a matsayin zababben shugaban kasar, to, zan tabbatar da cewa, Gbagbo zai sauka daga mukaminsa cikin kwarjini. Haka kuma, sanarwar ta ce, kungiyar AU da ta ECOWAS sun sake nuna goyon gaya ga Ouattara a matsayin sabon shugaban kasar, kuma dole ne Gbagbo ya mika mulki ga Ouattara cikin gaggawa, haka kuma sanarwar ta yi kira ga Gbagbo da Ouattara da su yi hakuri, don hana yanayin da ake ciki kara tabarbarewa, haka kuma, sanarwar ta ba da shawara ga kungiyar AU da ta ECOWAS, da su kara tura wata tawagar shugabanni daban zuwa kasar Cote D'ivoire don yin shawarwari da Gbagbo da Ouattara.

Kafofin yada labaru sun bayyana cewa, Gbagbo ya amince da warware rikicin da ake ciki cikin ruwan sanyi kuma ba tare da wasu sharudda ba, kuma wannan ya shaida cewa, ra'ayin Gbagbo ya samu sassauci, haka kuma, ya cika alkawarin da ya dauka, wato ya dage kawanyar da aka yi wa otel din da abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara ke da ofishinsa. Haka kuma, kasashen duniya sun gargadi Gbagbo da ya sauka daga mukaminsa, kasar Amurka ta bayyana cewa, za ta ba Gbagbo mafaka a kasarta, don kawo sassauci ga yanayin da ake ciki a kasar Cote D'ivoire. Haka kuma shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce, zai mika wani mukami na kungiyar kasashen duniya ga Gbagbo, haka kuma, majalisar gudanarwar ta Amurka ta ba da sanarwa, inda ta bayyana cewa, ta nuna goyon baya ga kokarin da kungiyar ECOWAS ta yi, kuma tana fatan Gbagbo zai sauka daga mukaminsa cikin kwarjini, kuma dukkan wadannan sun kawo wani sharadi na warware rikicin kasar Cote D'ivoire cikin ruwan sanyi.

Amma manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu tsugune ba ta kare ba, game da warware rikicin kasar Cote D'ivoire. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China