Sanarwar ta ce, ranar 3 ga wata, tawagar da ta hada firaministan kasar Kenya, shugabannin kasashen Benin, Saliyo, Cape Verd da shugaban kwamitin kungiyar ECOWAS ta isa Abidjan babban birnin kasar Cote D'ivoire domin shiga tsakanin matsalar kasar. Gbagbo ya nuna yarda wajen sulhunta wannan rikici ba tare da wani sharadi ba, kuma ya yi alkawari cewa, zai janye sojojin da ya jibga a waje da otel da tsohon firaministan kasar Ouattara ke ci.
Ban da wannan kuma, sanarwa ta ce, AU da ECOWAS sun sake jaddd goyon baya ga Ouattara a matsayin sabon shugaban kasar, kamata ya yi Gbagbo ya mikawa masa mulkin kasar tun da wuri. Dadin dadawa, sanarwa ta yi kira ga bangarori biyu na Ouattara da Gbagbo da su yi hakuri da juna domin hana tsanantar da halin da ake ciki.
An labarta cewa, ran 4 ga wata a Abuja, shugaban kasar Nijeriya dake rike da shugabancin karba-karba na ECOWAS Goodluck Jonathan ya jaddada cewa, idan Gbagbo bai mika iko ba ga Ouattara, to ECOWAS za ta dauki makakin soja bisa doka domin saukar da shi.(Amina)