in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe 4 na Afrika sun je kasar Cote d'Ivoire domin gudanar da aikin shiga tsakani
2011-01-04 10:40:25 cri

A ran 3 ga wata, shugabannin kasashen Benin da Saliyo da Cape Verde dake yammacin Afrika da kuma firaministan kasar Kenya Raila Amollo Odinga sun isa kasar Cote d'Ivoire domin gudanar da aikin shiga tsakani kan rikicin siyasa da ya abku bayan da aka kawo karshen babban zabe na kasar.

A wannan rana a birnin Abidjan, babban birnin kasar Cote d'Ivoire a fannin tattalin arziki, shugabannin kasashen 4 sun yi shawarwari tare da shugaban kasar Laurent Gbagbo, daga bisani kuma, suka yi shawarwari tare da mutumin da duniya ta yarda shi ne ya lashe zabe Ouattara. Yanzu, bangarori daban daban ba su fayyace sakamakon da suka samu a gun shawarwari ba.

A ran 2 ga watan Disamban bara, kwamitin babban zabe mai zanan kansa na kasar Cote d'Ivoire ya sanar da cewa, Ouattara ne ya lashe zaben. Amma a kashegari, kwamitin tsarin mulki na kasar ya sanar da soke wannan sakamakon zaben, kuma ya sanar da cewa, Laurent Gbagbo ne ya lashe zaben. Daga bisani, sun yi rantsuwar kama aikin shugabancin kasar daya bayan daya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China