Bisa labarin da ofishin firaminsitan kasar Kenya ya bayar, an ce, Odinga zai isa Abuja babban birnin kasar Nijeriya da farko domin tattaunawa kan yadda za a warware rikicin Cote D'ivoire tare da shugaban kungiyar ECOWAS kana da shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan. Daga baya, a matsayin wakilin neman sulhuntawa na kungiyar AU, Odinga zai je Cote D'ivoire domin shiga tsakani kan batun rikicin siyasar kasar tare da shugabannin kasashen Benin, Saliyo da Cape Verd.
An labarta cewa, a ran 27 ga watan Disamba na shekarar bara, AU ta nada Odinga a matsayin wakili a aikin shawo kan rikicin kasar Cote D'ivoire.(Amina)