Haka kuma Ban Ki-moon ya furta cewa, ya dora matukar muhimmanci kan rahoton da aka bayar kan keta hakkin bil Adam a kasar Cote d'Ivoire. Kuma ya ba da umurni ga tawagar da ke gudanar da ayyuka da MDD ta tura zuwa kasar wato UNOCI wajen daukar matakai dadai karfinta domin shiga cikin yankunan da aka ambata a cikin rahoton, a kokarin hana da kuma binciken yadda ake keta hakkin bil Adam.
An shirya babban zabe a kasar Cote d'Ivoire a watan Nuwamba na shekara ta 2010, inda tsohon shugaban kasar Lauren Gbagbo da kuma Alassane Ouattara, shugaban jam'iyyar adawa kuma tsohon firaministan kasar dukkansu suka sanar da lashe zaben, da kuma kafa gwamnatocinsu, ko da yake MDD da kungiyar EU da ta AU sun nuna goyon baya ga Mr. Ouattara.(Kande Gao)