in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya gargadi magoya bayan Gbagbo da su yi hakuri
2010-12-31 11:02:24 cri

A ran 30 ga wata, kakakin babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa, inda ya yi gargadi cewa, kada magoya bayan tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire wato kungiyar "kishin kasa" ta matasa su tada rikici, kuma ya yi kira da bangarori daban daban da su yi hakuri don tabbatar da dawamammen zaman lafiya a kasar.

Sanarwar ta yi magana kan shirin da kungiyar "kishin kasa" ta matasa ta yi na kai farmaki a ran 1 ga watan Janairu na shekara mai zuwa ga otel din Golf inda shugaba Ouattara ya sauka, ta ce, duk wani farmakin da za a kai wa otel din golf zai haddasa karin rikici, kana alamarin na iya kai ga sake tada yakin basassa a kasar. Kazalika, ya kalubalanci dukkan mutanen da ya shafa da kada su aikata wannan tarzoma mai hadari.

Mashawarcin Ban Ki-Moon mai kula da harkokin hana abkuwar kisan kiyashi Francis Deng da kuma mashawarci mai kula da harkokin kare hakkin dan Adam Edward Luck sun bayar da wata hadaddiyar sanarwa a ran 30 ga wata, inda suka nuna damuwa sosai kan yanayin da kasar Cote d'Ivoire ke ciki, kana sun nemi bangarori daban daban na kasar da su dauki nauyin kare jama'ar kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China