in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu tsugune ba ta kare ba a kasar Cote D'ivoire
2010-12-30 16:39:39 cri

Bayan da aka gudanar da zaben shugaban kasa a Cote D'ivoire a farkon wannan wata, an samu kasancewar shugabanni biyu a kasar. Ko da yake ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba kasa da kasa suka yi kokarin shiga-tsakani, amma shugaban kasar Laurent Gbagbo ba ya so ya sauka daga karagar mulki. Ranar 28 ga wata, kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta tura wata tawaga ta musamman zuwa kasar Cote D'ivoire don yin shiga-tsakani, amma ba ta cimma nasara ba saboda Gbagbo ya ki yin sassauci. Daga baya a ranar 29 ga wata, tawagar ECOWAS ta koma hedkwatarta dake Abuja, babban birnin kasar Najeriya. Amma duk da haka, Laurent Gbagbo ya amince da sake komawar tawagar kungiyar ECOWAS a farkon shekarar badi, a kokarin yin shawarwari dangane da halin da ake ciki a kasar Cote D'ivoire.

Ranar 28 ga watan Nuwamba, jagoran 'yan hamayya na kasar Cote D'ivoire Alassane Ouattara da shugaban kasar Laurent Gbagbo su ne suka kai ga zaben shugaban kasar zagaye na biyu. Sa'an nan a ranar 2 ga watan Disamba, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Cote D'ivoire ta sanar da cewa, Ouattara ne ya lashe zaben. Amma ranar 3 ga wata, hukumar ta yi watsi da wannan sakamako, inda ta ce Gbagbo ne ya lashe zaben, abun da ya sa wadannan mutane biyu suka sanar da kama aikin shugabancin kasar Cote D'ivoire.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China