in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar tarayyar kasashen yammacin Afrika ta gudanar da aikin shiga tsakani a karo na karshe kan halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire
2010-12-29 17:22:20 cri

Bayan da aka kammala babban zabe a kasar Cote d'Ivoire, shugaba mai ci na kasar Gbagbo da tsohon firaministan kasar Ouattara sun sanar da lashe zaben, kuma sun yi ratsuwar kama aiki daya bayan daya, sabo da haka, kasar Cote d'Ivoire ta shiga cikin halin kiki-kaka na "kasa daya shugabanni biyu". Domin kawo karshen wannan halin siyasa, kungiyar tarayyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afrika ta tura wata tawagar dake kunshe da shugabannin kasashen Benin da Saliyo da kuma Cape Verde zuwa kasar Cote d'Ivoire. A ran 28 ga wata, tawagar ta isa birnin Abidjan, babban birnin kasar a fannin tattalin arziki, kana ta yi shawarwari tare da shugaba mai ci Gbagbo da shugaban jami'iyyar adawa Ouattara.

A wannan rana, shugabannin kasashen Benin da Saliyo da kuma Cape Verde sun gana da wakilin babban sakataren MDD dake kasar Cote d'Ivoire Choi Yong-Jin, sannan kuma sun tafi fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Gbagbo, inda suka kwashe awoyi 3 suna shawarwari. Daga bisani kuma, sun je otel din golf dake birnin Abidjan domin ganawa da shugaban jam'iyyar adawa Ouattara. Bayan da aka kammala ayyukan wannan ziyara, shugabanni 3 ba su fayyace ba sakamakon da suka samu a wannan ziyararsu ta shiga tsakani.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China