Shugabannin 3 sun yi shawarwari tare da wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da harkokin kasar Cote d'Ivoire Choi Yong-jin da shugabannin kasar Cote d'Ivoire wato Gbagbo da Ouattara. Ya zuwa yanzu dai, ba a samu wani sakamako mai kyau kan shawarwarin ba.
A ran 2 ga wata, hukumar zaben kasar Cote d'Ivoire mai zaman kanta ta sanar da cewa, tsohon firaministan kasar Ouattara ya lashe zaben shugaban kasar. Kashe gari, kwamitin kundin tsarin mulkin kasar ya soke wannan sakamako, kana ya sanar da cewa, Gbagbo ya cimma nasara. A ran 4 ga wata, Gbagbo da Ouattara sun yi rantsuwar kama aiki bi da bi.(Zainab)