in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ouattara ya yi kira ga al'ummar kasar Cote d'Ivoire da su fara yajin aikin gama gari
2010-12-27 09:25:59 cri

Rahotannin da kafafofin watsa labarai suka bayar a ranar lahdi na cewa,jamiyyar Alassane Ouattara ta yi kira ga alummar kasar da su fara yajin aikin gama gari har sai Laurent Gbagbo ya sauka daga karagar mulki.

Rahotannin sun bayyana cewa, jamiyyar adawa ta RHDP ta ba da wata sanarwa inda ta bukaci jama'a da su fara yajin aikin daga ranar Litinin.

Kasar Cote d'Ivoire ta tsinci kanta cikin rikicin siyasa tun lokacin da aka gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ranar 28 ga watan Nuwamba.Dukkan mutanen biyu shugaba mai ci Gbagbo da shugaban 'yan adawa Ouattara sun yi ikirarin lashen zabe kana suka rantsar da kansu a matsayin shugaban kasar,sannan suka kafa gwamnatocinsu.

Gbagbo dai ya samu goyon bayan majalisar kundin tsarin mulkin kasar, yayin da Ouattara ya samu goyon bayan hukumar zaben kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China