in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi marhabin da shawarar da babban taron majalisar ya amince game da sabon wakilin dindindin na kasar Kodivwa a majalisar
2010-12-25 20:44:19 cri
Babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa a ranar 24 ga wata, inda ya yi marhabin da shawarar da babban taron majalisar ya amince da ita game da sabon wakilin dindindin na kasar Kodivwa dake majalisar, Youssouf Bamba.

Sanarwar ta ce, wannan muhimmin kudurin da aka tsaida ya nuna cewa, kasashen duniya su cimma matsayi daya wajen amince da sabuwar gwamnatin kasar Kodivwa karkashin shugabancin Alassane Ouattara.

Bayan haka kuma, a hakika dai wannan shawarar da aka yanke na nufin cewa, MDD ta amince da gwamnatin Ouattara. Yanzu Ouattara ya riga ya samu goyon-baya daga kungiyoyin AU, ECOWAS, gami da kungiyar tarayyar Turai EU.

Har wa yau kuma, a ranar 24 ga wata, kungiyar ECOWAS ta kara kira wani taron shugabanni na musamman a birnin Abuja na kasar Nijeriya, inda ta kalubalanci tsohon shugaban kasar Kodivwa, Laurent Gbagbo da ya mika mulki ta hanyar lumana ga tsohon firaministan kasar, Ouattara, wanda kuma ake ganin shi ne ya lashe zaben shugaban kasar.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka bayar bayan taron, an ce, kungiyar ECOWAS za ta aika da wata tawaga zuwa kasar Kodivwa, don kalubalantar Gbagbo da ya mika mulki ta hanyar lumana. Dadin dadawa, sanarwar ta yi gargadin cewa, idan Gbagbo bai amince da shawarar mika mulki ba, kungiyar za ta dauki matakan da ya hada da amfani da karfin makamai don tabbatar da ikon jama'ar kasar Kodivwa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China