A gun taron, mataimakiyar kwamishinan hukumar UNHRC Kyung-Wha Kang ta bayyana cewa, rukunin nazari kan hakkin bil Adam da M.D.D ta tura zuwa kasar Cote D'ivoire ya tabbatar da cewar yawan mutanen da suka mutu a sakamakon gallaza musu ya kai 173, an tsare mutane 471 a gidan kurkuku, kuma mutane 24 sun bace.
A ran 2 ga wata, hukumar babban zabe mai zaman kanta ta sanar da samun nasarar jam'iyyar adawa da gwamnatin da ke karkashin jagorancin tsohon firayim ministan kasar Ouattara a babban zaben. Kuma a ran 3 ga wata, kwamitin kula da tsarin mulkin kasar ya sanar da cewar tsohon shugaban kasar Gbagbo ya ci nasara a gun babban zaben. A ran 16 ga wata, an sheda fashin rikicin a tsakanin masu nuna goyon baya ga Ouattara da sojojin da ke karkashin jagorancin Gbagbo.(Abubakar)