A wannan rana kuma, Laurent Gbagbo ya yi jawabi ta telibijin, inda ya nuna cewa, yana mutunta tsarin mulkin kasar da shari'a, kuma yana maraba da a kafa wannan kwamitin. Gbagbo ya ce, kwamitin zai dauki nauyin binciken ayyukan zabe da kokarin magance abkuwar wasu matsaloli cikin lumana.
Ban da wannan kuma, Gbagbo ya nuna cewa, kamata ya yi, kwamitin ya mai da wakilan wasu kungiyoyi ciki har da AU, ECOWAS, kungiyar kasashen dake amfani da kudin Cefa a Afrika, kungiyar tarayyar kasashen Larabawa, MDD, EU, Amurka, Rasha da Sin a matsayin rukunin ba da jagoranci.(Amina)