A wannan rana kuma, Ban Ki-Moon ya yi wa taron MDD bayyani kan halin da kasar ke ciki na cewa, ya nuna damuwa sosai ga batun an dakatar da samarwa tawagar wasu kayayyakin da suke bukata, kuma ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi kokarin ba da tallafi ga kungiyar.
A wannan rana a hedkwatar MDD, mataimakin sakatare mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na majalisar Alain Le Roy ya bayyana cewa, yanzu Cote D'ivoire na cikin hali mafi tsanani. Bisa labarin da aka bayar an ce, magoyon Laurent Gbagbo sun fara kawo cikas ga ayyukan tawagar, alal misali, sun tilastawa wasu kamfanoni da su dakatar da samarwa tawagar kayayyakin da suke bukata tare da korar wasu ma'aikatan tawagar daga gidajensu da sauransu. Roy ya yi kira da su daina kai barazana ga ma'aikatan MDD.
An labarta cewa, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta sanar da hana shugaban kasar Cote D'ivoire Laurent Gbagbo da iyalansa shiga kasar Amurka a wannan rana.(Amina)