A wannan rana, kwamitin sulhu ya yi wani taro kan yanayin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire, inda aka yanke shawarar tsawaita wa'adin kungiyar MDD a kasar zuwa ran 30 ga watan Yuni na badi. A sa'i daya, da babbar murya ne kwamitin sulhu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Cote d'Ivoire a ran 18 ga wata, kuma ya yi gargadi cewa, za a yanke hukunci ga duk wadanda suka kai hari ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD da fararen hula.
A ran 2 ga wata, kwamitin harkokin zabe mai zaman kansa na Cote d'Ivoire ya sanar da cewa, shugaban kungiyar adawa Ouattara ya ci babban zaben shugaban kasar. A ran 3 ga wata, kwamitin kundin tsarin mulkin kasar Cote d'Ivoire ya shelanta cewa, shugaban kasar Laurent Gbagbo ya ci wannan zabe. Mutanen biyu sun yi rantsuwar kama aiki a ran 4 ga wata. Daga bisani, an fara yin rikice-rikice a kasar. MDD da kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar tarayyar Turai suna nuna goyon baya ga Ouattara.(Fatima)