in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin raya tattalin arziki maras gurbata muhalli
2010-12-20 22:18:24 cri
Ibrahim: A ran 27 ga watan Nuwamba, an rufe bikin nune-nunen sana'o'in marasa gurbata muhalli da fasahohin zamani masu kiyaye ingancin yanayin duniya na shekarar 2010 a nan birnin Beijing. Kamfanoni fiye da 200 wadanda suka fito daga kasashe da yankuna 25, kuma suka shahara a duniya sun halarci wannan taro, inda suka nuna wa 'yan kallo sabbin fasahohin zamani da kayayyaki masu kiyaye ingancin muhalli kuma masu fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya kadan.

Sanusi: A cikin kamfanoni 212 wadanda suka halarci wannan biki, kamfanonin kasashen waje sun kai kashi 60 cikin kashi dari. Kamfanin Total na kasar Faransa na daya daga cikin kamfanonin man fetur na 4 mafi girma a duniya. Mr. Xu Zhonghua, wakilin kimiyya na farko na kamfanin Total dake nan kasar Sin ya bayyana cewa, kamfanin Total ya ga yadda kasar Sin ta yi gyare-gyare kan tsarinta na tattalin arziki da bude kofarta ga kasashen waje, kuma ya ga yadda kasar Sin ke kokarin raya tattalin arziki mai kiyaye muhalli. Mr. Xu yana mai cewa, "Kamfanin Total ya kasance a kasar Sin har na tsawo kusan shekaru 31. sabo da haka, mu kan fadi cewa, mun ga yadda kasar Sin ta yi gyare-gyare kan manufofinta na tattalin arziki da bude kofarta ga kasashen waje. Yawan man gas, wato makamashi mai tsabta da muke fitar zuwa kasar Sin a kowace shekara ya kai kashi 10 cikin dari bisa na jimillar man gas da kasar Sin ke shigowa da shi daga kasashen waje. Gwamnatin kasar Sin na mai da hankali sosai kan fasahohin zamani wadanda suke iya tabbatar da samun ci gaba ba tare da cikas ba, sannan ta zuba makudan kudi da mutane masu tarin yawa kan yadda za a iya samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba."

Ibrahim: Haka ne. Kamar yadda Mr. Xu ya furta, a cikin shekaru 5 da suka gabata kawai, gwamnatin kasar Sin ta kebe kudin Sin yuan biliyan 200 kan ayyukan tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Wadannan kudin da aka kebe ya sa aka zuba kudin Sin yuan biliyan dubu 2 kan irin wadannan ayyuka.

Sanusi: Lokacin da ake kaddamar da wannan bikin nune-nunen sana'o'i marasa gurbata muhalli da fasahohin zamani masu kiyaye ingancin yanayin duniya na shekarar 2010, Mr. Jiang Yaoping, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana son yin amfani da wannan biki da ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya ta fuskar bunkasa tattalin arziki maras gurbata muhalli. Mr. Jiang ya bayyana cewa, "A gun wannan biki, an yi nune-nunen fasahohin zamani na yin amfani da makamashi mai tsabta da na tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da na tsabtace muhalli da na fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya kadan da na raya tattalin arzikin bola jari da dai makamatansu. Gwamnatin kasar Sin tana fatan kara yin hadin gwiwa da yin mu'amala da sauran kasashen duniya ta fuskar bunkasa tattalin arziki maras gurbata muhalli a kokarin neman hanyoyi masu dacewa na tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya."

Sanusi: Niyya da kokarin da kasar Sin ta nuna wa sauran kasashen duniya a fannonin bunkasa tattalin arziki maras gurbata muhalli da fasahohin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya sun sa kamfanonin jarin kasashen waje sun samu imani ga kasar Sin. Kamfanin Martec na kasar Canada wani kamfani ne dake kan gaba wajen gyara hanyoyin mota. Injunan da wannan kamfani ya kera sun iya tsimin kudin gyara hanyoyin mota da kashi 70 cikin kashi dari. Mr. Mostafa Joharifard, shugaban hukumar direktocin wannan kamfani ya bayyana cewa, "A ganina, kasar Sin wata kasuwa ce mafi kyau a duniya. Kasar Sin ta riga ta shaida wa sauran kasashen duniya cewa, tana mai da hankali sosai wajen bunkasa tattalin arziki maras gurbata muhalli. A kan batun bunkasa irin wannan tattalin arziki, yawan kudin da kasar Sin ta zuba ya fi na kowace kasa yawa. Wannan biki ma ya shaida matsayin da kasar Sin ke dauka."

Ibrahim: Sabo da gwamnatin kasar Sin na mai da hankali sosai wajen raya kasar Sin da za ta zama wata kasa mai tasiri, inda ake tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli kamar yadda ya kamata, yanzu kamfanonin kasar Sin suna kuma kara saurin canja hanyoyin neman ci gaba, wato sun fi mai da hankali kan nazari da kuma fitar da kayayyaki masu tsimin makamashi kuma masu kiyaye muhalli. Har ma wasu hukumomin kudi sun kafa asusun ba da tallafin kudi ga fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli. Mr. Zhu Ping, mai ba da shawara ga kamfanin bankin Beijing ya bayyana cewa, "Wasu kananan kamfanoni suna da fasahohin zamani na raya tattalin arziki maras gurbata muhalli, amma ba su da isashen kudin da suke bukata. Sabo da haka, mun tsai da kudurin ba su tallafin kudi."

Sanusi: Gwamnatin kasar Sin ta kuma bayyana cewa, za a ci gaba da nuna goyon baya ga masana'antu da fasahohin zamani marasa gurbata muhalli a nan gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China