Yayin da yake hira tare da manema labarai a wannan rana, kakakin dakarun MDD dake jibge a Cote D'ivoire ya ce, tawagarsa ba ta taba samar da goyon-bayan makamai ga duk wata kungiya ba, kuma tana nuna matsayinta na kasancewa tsaka-tsakiya.
Wannan kakaki ya kuma jaddada cewa, kungiyar MDD zata ci gaba da daukar nauyin shimfida zaman lafiya a kasar Cote D'ivoire, da nuna goyon-baya ga jama'ar kasar da su lalubo bakin zaren daidaita rikicin siyasar kasar yadda ya kamata.
Ranar 18 ga wata, Mista Laurent Gbagbo ya bada sanarwa ta kafar telebijin inda ya bukaci sojojin kasa da kasa da su janye daga kasarsa.(Murtala)