in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya nuna damuwa kan farmaki da aka baiwa ma'aikatan kiyaye zaman lafiya dake Kodivwa
2010-12-19 17:49:32 cri
Babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa a ranar 18 ga wata, inda ya nuna damuwa sosai game da farmakin da aka kaiwa ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD a wannan rana a kasar Kodivwa, kana ya jaddada cewa, duk wani farmakin da aka kai wa sojojin MDD tamkar farmaki ne da aka kai wa kasashen duniya.

Ban Ki-Moon ya bayyana a cikin sanarwar cewa, ba za a amince da duk wasu ayyukan dake da nufin hana aikin MDD ba, kuma tilas ne a dauki wasu matakai kan wannan batu. Ya kara bayyana cewa, tawagar MDD dake kasar Kodivwa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta a kasar, inda za su sa ido da rubuta duk miyagun ayyukan dake da nasaba da take hakkin bil Adam, da tayar da duk wani aikin nuna karfin tuwo, da kuma kai farmaki kan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, da dai sauransu.

A sa'i daya kuma, Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, sanarwar da kungiyar ECOWAS, da kungiyar AU suka bayar sun nuna cewa, kasashen Afrika na nuna girmamawa ga jama'ar kasar Kodivwa, kuma sun amince da tsohon firaministan kasar, Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasar, sanarwar kuma ta samu goyon baya daga kwamitin sulhu na MDD.

Bisa wani labari na daban da aka bayar an ce, shugaban kasar Kodivwa, Laurent Gbagbo ya bayar da wata sanarwa ta gidan talibiji na gwamnatin kasar a ranar 18 ga wata, inda ya bukaci tawagar MDD dake kasar, da rundunar sojojin kasar Fransa da su janye jiki daga kasar Kodivwa.

Kakakin gwamnatin Laurent Gbagbo ya ce, gwamnatin kasar Kodivwa na ganin cewa, tawagar MDD ta nuna gazawa a cikin ayyukanta, kuma sun dauki wasu matakai ba bisa adalci ba. Tawagar kuma ta bayar da makamai ga magoyan bayan tsohon firaministan kasar Kodivwa.

A ranar 2 ga wata, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kodivwa ta sanar da cewa, tsohon firaministan kasar, Alassane Ouattara ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi. Amma, a ranar 3 ga wata, kwamitin tsarin mulki na kasar ya soke wannan sakamakon zabe, kuma ya shelanta cewa, Laurent Gbagbo ne ya yi nasara. Bayan haka kuma, mutanen biyu kowanne ya yi rantsuwar kasancewa shugaban kasar a ranar 4 ga wata. Yanzu, MDD, kungiyar AU, da kuma kungiyar EU dukkansu suna goyon bayan Alassane Ouattara a matsayin wanda jama'ar kasar suka zaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China