A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Ban Ki-moon ya ce, aikin gaggawa yanzu shi ne a hana ayyukan da za su iya kara tsananta halin da ake ciki a kasar Cote d'Ioivre. Tuni ECOWAS da AU sun bayyana matsayinsu na girmama wa tsarin mulkin kasar da burin jama'a, kuma abin da MDD ke son bayyana shi ne, sakamakon zabe ya bayyana kome, babu sauran hanyoyin da za a iya zaba.
Sa'an nan, Ban Ki-moon ya matsa wa Laurent Gbagbo kaimin sauka daga karagar mulki tare kuma da mika mulki ga abokin hamayyarsa.
Har wa yau, a ranar 17 ga wata, majalisar gudanarwa ta Amurka ta ce, abu ne na haram da Gbagbo ya ci gaba da rike da ragamar mulki, idan har ya ki sauka daga mukaminsa, lallai, Amurka na shirin kakaba takunkumi gare shi tare kuma da magoya bayansa.(Lubabatu)