A ran 31 ga watan Nuwanba, kasar Cote d'ivoire ta gudanar da babban zaben shugaban kasar a zagaye na biyu. Kwamitin kula da babban zaben mai zaman kansa ya sanar da cewar shugaban jam'iyyar adawa da gwamnatin kasar kuma tsohon firayim ministan kasar Alassane Dramane Ouattara ya ci nasara, kuma M.D.D da kungiyar AU da kungiyar ECOWAS sun nuna goyon baya ga sanarwar da kwamitin ya bayar. Amma, a ran 1 ga wata, kwamitin kula da tsarin mulkin kasar Cote d'ivoire ya ki amincewa sanarwar da kwamitin ya bayar, kuma ya sanar da cewar shugaban kasar Laurent Gbagbo ya ci nasara. Saboda haka, Laurent Gbagbo da Alassane Dramane Ouattara kowa daga wajensa ya ce shi ya samu nasara, kuma sun kafa gwamnatinsu bi da bi, ta haka, kasar ta kasance da shugabanni 2.