in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi musayar wuta a waje da otel da shugaban jam'iyyar adawa ta kasar Cote d'Ivoire ke ciki
2010-12-17 09:43:02 cri

A ran 16 ga wata a birnin Abidjan, an yi musayar wuta a tsakanin masu goyon bayan shugaban jam'iyyar adawa ta kasar Cote d'Ivoire kuma tsohon firaministan kasar Alassane Ouattara da sojojin dake karkashin jagorancin shugaban yanzu na kasar Laurent Gbagbo, wadda ta haddasa mutuwar mutane a kalla 4.

A wannan rana da safe a waje da otel da Ouattara ke zauna, masu goyon bayansa sun yi musayar wuta tare da sojojin shugaba Gbagbo yayin da suke tafiya zuwa gidan telebijin na kasar, wadda ta haddasa mutuwar mutane a kalla 4. A ran 14 ga wata da dare, tawagar MDD dake kasar ta bayar da wata sanarwa, inda ta ce, kawancen jam'iyyun adawa mai goyon bayan Ouattara zai yi zanga-zanga a ranar 16 da ta 17 don aza sabon darektan gidan telebijin na kasar da kuma kai sabon firaministan kasar fadarsa.

A ran 16 ga wata da safe, masu goyon bayan Ouattara sun yi zanga-zanga zuwa gidan telebijin na kasar, kafin 'yan sanda sun tarwatsa su, abun da ya haddasa mutuwa da raunata mutane da dama.

A ran 16 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taro game da kasar Cote d'Ivoire, inda aka saurari rahoton da mataimakin sakataren kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na MDD Alan Le Rov ya gabatar. Kana kwamitin sulhu na MDD ya yi tir da rikicin da ya abku a kasar Cote d'Ivoire.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China