in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Kodivwa da su yi hakuri
2010-12-16 16:54:18 cri

A ranar 15 ga wata, babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa, inda ya nuna damuwa ga mawuyacin hali da kasar Kodivwa ke ciki ta fuskar siyasa, kuma ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar da su yi hakuri da juna don magance yunkurin yakin basasa.

A cikin sanarwar kuma, Ban Ki-Moon ya kara yin kira ga Laurent Gbagbo da ya nuna girmamawa ga ra'ayin jama'ar kasar, da kuma mika mulki ga Alassane Ouattara da ya ci zaben shugaban kasar. Dadin dadawa, ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi mu'ammala tare da shugabannin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, don kawar da rikicin siyasa ta hanyar lumana.

Ana ta kara samun tsanancewar yanayi a kasar Kodivwa sakamakon shugabanni biyu dake ikirrarin rike mulki a cikin kasar. Tawagar MDD dake kasar ta bayyana cewa, rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kara sintiri a sama da kasa, don tabbatar da tsaron kasar.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China