A cikin sanarwar kuma, Ban Ki-Moon ya kara yin kira ga Laurent Gbagbo da ya girmama ra'ayin jama'ar kasar, da kuma mika mulki ga Alassane Ouattara da ya ci zaben shugaban kasar. Dadin dadawa, ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi mu'ammala tare da shugabannin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, don kawar da rikicin siyasa ta hanyar lumana.
Ana ta kara samun tsanancewar yanayi a kasar Kodivwa sakamakon shugabanni biyu da kowanne ke ikirrarin kasancewa shugaba a kasar. Tawagar MDD dake kasar ta bayyana cewa, rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kara sintiri a sama da kasa, don tabbatar da tsaron kasar.
A ran 2 ga wata, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kodivwa ta sanar da cewa, tsohon firaministan kasar, Alassane Ouattara a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasar. Amma a ranar 3 ga wata, kwamitin tsarin mulkin kasar ya sanar da soke sakamakon da hukuma ta bayar, kana ya ce, shugaban kasar na yanzu Laurent Gbagbo ya lashe zaben. A ranar 4 ga wata, mutanen biyu sun yi rantsuwar kama aiki daya bayan daya, a ranar 5 ga wata kuma, dukkansu sun sanar da sunayen ministocin sabbin gwamnatocinsu, al'amarin da ya janyo wani kace-nace. MDD, da kungiyar AU, da kungiyar EU, da kuma sauran kungiyoyin duniya sun nuna goyon baya ga Alassane Ouattara.