in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan siyasa na kasashen Afirka suna fatan za a warware rikicin kasar Cote d'Ivoire yadda ya kamata
2010-12-14 09:24:23 cri

A ran 13 ga wata, 'yan siyasa da dama na kasashen Afirka sun nuna fatan ganin bangarori daban daban na kasar Cote d'Ivoire sun girmama sakamakon zaben shugaban kasar, da kuma warware rikicin zaben yadda ya kamata.

Tsohon firaministan kasar Togo Edem Kodjo dake halartar taron tunawa da shekaru 50 da babban taron MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1514 game da ikon samun 'yancin kasashe daga mulkin mallaka da shugaban kwamitin kungiyar AU Jean Ping da jami'in kula da harkokin zaman lafiya da tsaro na kwamitin Ramtane Lamamra sun bayyana wa 'yan jarida cewa, nahiyar Afirka tana bukatar zaman lafiya don samun ci gaba, amma ba ta bukatar rikicin da zaben shugabannin a kasashen ke haddasawa. Suna fatan bangarori daban daban na kasar Cote d'Ivoire za su girmama sakamakon zaben shugaban kasar, da kuma warware rikicin zaben yadda ya kamata. Kana kungiyar AU za ta yi kokari don cimma wannan buri.

A ran 13 ga wata a birnin Abidjan dake kasar Cote d'Voire, dakaru masu goyon bayan tsohon firaministan kasar Alassane Ouattara da sojojin gwamnatin kasar dake karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo sun yi musayar wuta, ya zuwa yanzu, babu wanda ya mutu ko jin rauni.

A ran 13 ga wata, ministocin harkokin waje na kasashe membobin kungiyar EU sun zartas da wata sanarwa, inda aka sanar da daukar matakan kayyade takardun visa da hana amfani da kudi ga shugaban kasar Cote d'Voire Laurent Gbagbo tare da masu goyon bayansa.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China