in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauyin da ake samu a tsakanin manufofin gwamnatin kasar Sin da zaman rayuwar jama'a
2010-12-13 14:14:58 cri
Ibrahim: Yanzu mun shiga watan karshe na shekarar 2010. A cikin wannan shekara daya, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufofi da yawa da suke da nasaba da inganta zaman rayuwar jama'a. Alal misali, manufofin dake da nasaba da kasuwar samar da gidaje da kiwon lafiya da gidajen renon kananan yara da kuma ma kula da tsoffi.

Sanusi: A farkon shekarar 2010, Mr. Wang Zhengjun, wanda ya yi shekaru 3 yana aiki ya yi fatan ya sayi wani gida a nan birnin Beijing domin aure. Dalilin da ya sa saurayi Wang ya tsai da wannan kuduri na sayen wani gida shi ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da jerin sabbin manufofin rage saurin karuwar farashin gidaje a karshen bara. Wang Zhengjun ya yi tsammanin cewa, tabbas ne farashin gidaje zai ragu a shekarar 2010. Amma ba zato ba tsammani, farashin gidaje ya kai matsayin koli a karshen watan Maris na bana. Sakamakon haka, Mr. Wang ya nuna damuwa sosai. Yana mai cewa, "Kudin da muke samu a kowane wata bai kai kashi daya na kudin da ake bukata ba na sayen gida, balle an yi maganar biyan jimillar kudin wannan gida baki daya. Sabo da haka, idan har farashin gida ya ci gaba da karuwa kamar haka, hakika ba za mu iya yin kome ba, sai dai mu zauna a nan kawai."

Ibrahim: Tun daga watan Afrilu na bana, gwamnatin kasar Sin ta kara daukar matakan sa ido kan kasuwar gidaje. Alal misali, idan wani mutum wanda yake da gida daya yanzu yana son sayen wani gida daban, to, yawan kudin da zai biya kamfanin sayar da wannan gida ba zai yi kasa da rabin kudin wannan gida ba. Sakamakon haka, saurin karuwar farashin gida ya soma raguwa a kasar Sin. Yanzu Mr. Wang ya dan kwantar da hankalinsa, ya bayyana cewa, "Mai yiyuwa ne zan iya sayen wani gida a badi. Ina ganin, har yanzu farashin gida ya yi tsada, mai yiyuwa zai ragu a shekara mai kamawa."

Sanusi: Mr. Wang Zhengjun ya damu sosai game da farashin gidaje, amma dattijo Cheng Wanhe, mai shekaru 75 da haihuwa wanda ke zaune a birnin Heze na lardin Shandong, wanda ya kamu da ciwon ido yau shekaru 2 da suka gabata, ya yi farin ciki sosai yanzu. A kwanakin baya, an yi masa aiki a idon kyauta. Sabo da haka, yanzu yana iya kallon kome da kome. Dattijo Cheng Wanhe yana mai cewa, "Gwamnatinmu na kula da mu sosai. Ba ma kawai an yi mini aiki kyauta ba, har ma ta ba mu kyakkyawar hidima. Ina farin ciki kwarai."

Ibrahim: A hakika dai, muhimman abubuwan da jama'ar kasar Sin za su yi farin ciki a nan gaba su ne, tun daga shekarar bara, gwamnatin kasar Sin ta soma yin gyare-gyare kan manufofin kiwon lafiyar jama'a. Kuma za ta kebe wa hukumomin kiwon lafiya kudin da yawansa zai kai kudin Sin yuan biliyan 850 a cikin shekaru 3 masu zuwa a kokarin kafa wani tsarin kiwon lafiya da zai shafi yawancin jama'ar kasar Sin.

Sanusi: Mr. Chen Zhu, ministan kiwon lafiya na kasar Sin ya ce, za a ci gaba da yin kokarin kula da lafiyar jama'a. Mr. Chen Zhu ya bayyana cewa, "Mukasudin yin wannan gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya shi ne muna son cimma wani buri a fannoni biyu, na farko shi ne a kokarin tabbatar da ganin cewa jama'a sun kasance cikin koshin lafiya a kullum. Sannan, idan kuma har wani mutum ya kamu da wani ciwo, za mu yi kokarin tabbatar da ganin an kai shi asibiti, kuma sun iya samun jinya kamar yadda ya kamata."

Ibrahim: Lokacin da jama'ar kasar Sin suke jin dadin manufofin yin gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya da aka aiwatar, a bangare guda kuma, sun soma nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyaki. Wannan al'amari ya fara ne a karshen rabin shekarar bana. Ba ma kawai wannan al'amari ya kawo illa ga wadanda suke samu kudi kadan ba, har ma ya kawo illa ga wadanda suke aiki a ofisoshin gwamnati.

Sanusi: Madam Zhang Bin wata babbar jami'a ce ga wani otel a nan Beijing, mijinta ma wani injiniya ne dake aiki a wani babban kamfanin jari kasashen waje. Jimillar albashinsu ta kai fiye da kudin Sin yuan dubu 20 a kowane wata, wato kimanin Naira dubu 350 a kudin Naira. Madam Zhang Bin ta kan adana rasidin kudin kayayyakin da ta saya. Ta nuna wa wakilinmu kananan takardu guda biyu domin bayyana sauyin farashin kayayyaki da aka samu cikin shekaru 2 da suka gabata. Madam Zhang ta ce, "Farashin lita biyar na man girki ya kai kusan kudin Sin yuan 50 a shekarar 2009, amma yanzu, farashi na lita biyar na man girki na kowane lita biyar ya riga ya kai kudin Sin 85 da wani abu, wato ya karu da kashi 70 cikin kashi dari."

Ibrahim: A kan samu sauye sauye a duniya a wannan lokaci, balle a nan kasar Sin. Jama'ar kasar Sin ma za su ci gaba da fuskantar sauye-sauye iri daban daban a nan gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China