A gun wani taron daidaita batun rigingimu a kasashen Afrika na AU da aka yi a birnin Algiers, Lamamra ya ce, AU tana ci gaba da dukufa kan fitar da wani matakin maido da dimokuradiyya da zaman lafiya a Cote D'ivoire. Kuma AU ta amince da nasarar tsohon firaministan kasar kuma shugaban jam'iyyar RDR Alassane Ouattara a zaben shugaban kasar, kuma ta yanke shawarar dakatar da Cote D'ivoire daga kungiyar AU cikin gajeren lokaci.
An labarta cewa, a ran 28 ga watan Nuwamba, Cote D'ivoire ta kada kuri'ar zaben shugaban kasa zagaye na biyu. Kuma a ran 2 ga wata, kwamitin zabe mai zaman kansa ya sanar da Ouattara a matsayin wanda ya lashe zabe da kashi 54.1 bisa 100, amma a ranar 3 ga wata, kwamitin tsarin mulkin kasar ya sanar da Laurent Gbagbo shugaban kasar mai ci a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 51.45 cikin 100. A ranar 4 ga wata, mutanen biyu sun yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar, hakan ya hadasa hadarin siyasa mai tsamani a kasar.(Amina)