in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin harhada magunguna na Hualiketai na Beijing na samun saurin ci gaba a Afirka
2010-12-10 20:38:36 cri

Kawo yanzu, an kammala aikin jefa kuri'a ta hanyar Intanet dangane da gasar fidda manyan kamfanonin kasar Sin 10 wadanda suka bayar da babbar gudummawa wajen karfafa zumunci tsakanin Sin da Afirka, wadda kungiyar sada zumunta tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka, da gidan rediyon CRI, gami da mujallar Afirka suka shirya tare. A kuri'un da aka kada, kamfanin harhada magunguna na Hualiketai na Beijing dake kan gaba ya kasance kamfanin harhada magunguna daya tilo, kuma babban aikin da yake kokarin tafiyarwa shi ne harhadawa gami da sayar da magungunan yaki da cutar malariya. Ranar 17 ga watan Nuwamba, shugaban wannan kamfani Lu Chunming ya kai ziyara gidan rediyon CRI, inda ya bayyana labarinsa na ceto mutane a Afirka.

A cikin wannan shiri, Mista Lu Chunming ya bayyana yadda kamfaninsa ke samun ci gaba da halin da ake ciki yanzu, haka kuma ya bayyana labarai masu ban sha'awa game da Afirka. Mista Lu ya ce, aikin da kamfaninsa ke kokarin gudanarwa, aiki ne na tallafawa mutane, wanda ke da babbar ma'ana kwarai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China