in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kamfanin CNMC ya bayyana ma'anar zumunci mai zurfi da ke tsakanin Sin da Afirka
2010-12-10 18:43:08 cri

Yanzu haka, hadaddiyar kungiyar sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta kasashen Afirka, da gidan rediyon kasar Sin na CRI, hade da mujallar Afirka suna kokarin shirya kada kuri'a don fitar da manyan kamfanoni 10 na kasar Sin wadanda za a ba su lambar yabo dangane da yadda suka ba da gudummawa wajen sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka. A bisa wannan yanayin da ake ciki ne, a ranar 17 ga watan Nuwamba, Luo Tao, shugaban kamfanin sarrafa ma'adinai na kasar Sin CNMC ya halarci wani shiri mai taken 'duba duniya kafin sauran mutane su yi'na CRI online wato kamfanin da ke kula da shafin yanar gizo na rediyon CRI, inda Mista Luo ya bayyana yadda kamfaninsa ya fara gudanar da aiki a nahiyar Afirka, har ma ya burge nahiyar a karshe.

Kamfanin CNMC ya fara shiga kasuwannin kasashen Afirka ne a shekarar 1996 bisa shiga wata takarar neman kwangila, abin da ya sanya kamfanin cikin jerin kamfanonin kasar Sin na farko da suka fara shiga kasuwannin Afirka bayan kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida hade da bude kofa ga kasashen waje. Sa'an nan, cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, daya bayan daya, kamfanin CNMC ya bude masana'antu 9 a kasashen Zambia da Congo, da kafa wani dandali na shirya hadin kai a tsakanin kasa da kasa, wato wani yanki na hadin ka tsakanin Zambia da Sin ta fuskar cinikayya da tattalin arziki, haka kuma ya kafa wata babbar rijiyar hakar dutsen tagulla hade da wata ma'aikatar tace ma'adinin tagulla. Cikin wannan shiri na CRI online, Luo Tao ya bayyana yadda kamfanin CNMC yake kokarin raya harkokinsa a Afirka, da kuma labaran ma'aikatan kamfanin masu sosa rai. Luo ya ce, ko wane ma'aikacin kamfanin da ke aiki a Afirka na da wani tarihi na nuna jaruntaka, gudunmawar da suke bayarwa ta bayyana ainihin ma'anar "zumunci mai zurfi da ya kasance a tsakanin Sin da Afirka". (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China