in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CMEC na kasar Sin na kokarin bayar da gudummawarsa wajen raya tattalin arzikin kasashen Afirka
2010-12-10 21:03:24 cri

A halin yanzu, ana kokarin gudanar da wani aiki na fidda manyan kamfanonin kasar Sin 10 wadanda suka bayar da babbar gudummawa ga karfafa dankon zumuncin tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wanda kungiyar sada zumunci tsakanin jama'ar kasashen Sin da Afirka da gidan rediyon CRI suka dauki nauyin shiryawa. Kawo yanzu, an riga an kammala mataki na farko na zabar wadannan kamfanoni. A cikin wannan mataki na farko, kamfanin shige da ficen manyan injunan gine-gine na kasar Sin , wato kamfanin CMEC shi ke kan gaba. Ya kasance a matsayin babban kamfanin masana'antu da cinikayya na farko a nan kasar Sin dake shige da ficen injunan injiniya, yaya ya shiga kasuwar kasashen Afirka? Kuma yaya wannan kamfani ya yi nasarar sada zumunci a tsakaninsa da kasashen Afirka? A kwanan baya, Mr. Jin Chunsheng, mataimakin shugaban wannan kamfani ya kawo ziyara gidan rediyon CRI, inda ya bayyana wa masu karanta shafinmu na Intanet yadda kamfaninsa yake neman ci gaba a kasashen Afirka.

Kamfanin CMEC na kasar Sin wanda ya shahara sosai a duniya ta fuskar neman kwangiloli. Tun daga shekaru 70 na karnin da ya gabata, ya soma neman kwangilolin tallafawa kasashen Afirka. Musamman a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, ya samu ci gaba sosai a kasuwannin kasashen Afirka.

Lokacin da yake ganawa da wakilinmu, Mr. Jin Chunsheng ya nuna mana wasu muhimman ayyukan da kamfaninsa ya yi a kasashen Afirka, alal misalai, tashar samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin ruwa da ya gina a kasar Congo Brazaville da tasoshin rarraba wutar lantarki da ya gina a kasar Angola da babban ginin rediyo da talibijin da ya gina a kasar Gabon. Wadannan muhimman ayyukan yau da kullum da suke da nasaba da muhimman sana'o'in wadannan kasashen Afirka sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautata halin da ake ciki a wadannan kasashe da kuma inganta rayuwar jama'a, kuma sun zama wani kyakkyawan tushe ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka. Lokacin da ya tabo dalilin da ya sa kamfaninsa ya samu wannan kyakkyawan maki a gun wannan bikin zaben nagartattun kamfanonin kasar Sin 10 da gidan rediyon CRI ya shirya, Mr. Jin Chunsheng ya ce, "makasudin samar da irin wadannan muhimman ayyukan yau da kullum a kasashen Afirka shi ne, muna son bayar da gudummawarmu wajen kafa wani kyakkyawan tushen raya tattalin arziki da kuma kyautata ingancin rayuwar jama'ar kasashen Afirka a kai a kai." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China