A cikin sanarwar da aka bayar bayan taron, an ce, kungiyar AU za ta ci gaba da neman hanyoyin warware rikicin siyasa na kasar Cote d'Ivoire cikin lumana bisa kudurin da aka tsaida.
Ban da wannan kuma, sanarwar ta kalubalanci tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da ya dora muhimmanci kan moriyar kasarsa har ma a nahiyar Afirka, da girmama sakamakon zaben, da kuma mika iko ga tsohon firaministan kasar Alassane Ouattara ba tare da bata lokaci ba.(Zainab)