in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na goyon bayan Alassane Quattara a matsayin shugaban kasar Cote d'Ivoire
2010-12-09 10:53:39 cri

Ran 8 ga wata, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya bayar da sanarwa, inda ya yi kira ga bangarori daban daban da su yarda da sakamakon babban zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire da aka yi, inda tsohon firaminista Alassane Quattara ya zama sabon shugaban kasar, kuma ya yi Allah wadai kan wadanda ke kokarin mai da hannun agogo baya tun bayan fitar da sakamakon zaben.

Wannan sanarwa ta jaddada cewa, kwamitin sulhu zai hukunta duk wanda zai kawo cikas ga yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Cote d'Ivoire, ko kawo cikas ga ayyukan majalisar dinkin duniya a kasar, ko keta hakokin bil-adam.

A ran 2 ga wata, kwamitin babban zabe na kasar Cote d'Ivoire ya sanar da Mr. Alassane Quattara shugaban jam'iyyar adawa kuma tsohon firaminista a matsayin wanda ya lashe babban zabe. Amma, a ran 3 ga wata, kwamitin tsarin mulkin kasar ya sanar da yin watsi da kuri'un da aka jefa a birane 7 da ke arewancin kasar, ya ce shugaba Laurent Gbagbo na yanzu ya lashe babban zabe. Ran 4 ga wata, mutane biyu ko wanensu ya yi rantsuwar kama aiki daban daban, wannan ya jawo hankalin kasashen duniya sosai. Ran 7 ga wata, kungiyar ECOWAS ta bayar da sanarwa, inda ta nuna goyon baya ga Quattara a matsayin shugaban kasar, kuma ta kalubalanci Gbagbo da ya mika iko cikin sauri. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China