Goodluck Jonathan ya fadi haka bayan da ya yi shawarwari da takwarorinsa na Senegal, Togo, Ghana, Liberiya, Burkina Faso, da kuma tsohon shugaban kasar Mali.
A wannan rana, shugabannin kasashe 7 na kungiyar ECOWAS sun fitar da wata sanarwa bayan sun kira taron gaggawa. A karshe shugabannin sun jaddada goyon bayansu ga Ouattara a matsayin sabon shugaban kasar Cote d'Ivoire, tare da matsa lamba ga shugaban kasar Laurent Gbagbo da ya amince da sakamakon zabe zagaye na biyu ta hanyar mika mulkin kasar tun da wuri.(Fatima)