Bayan haka kuma, Ban Ki-Moon ya kara yin kira ga jama'ar kasar da su tabbatar da samun natsuwa da kwanciyar hankali, kana kuma ya jaddada cewa, kungiyar musamman ta MDD dake kasar Kodivwa za ta yi iyakacin kokari bisa iznin da ta samu don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
A ranar 4 ga wata a fadar shugaban kasar Kodivwa, shugaban kasar, Laurent Gbagbo ya yi rantsuwar kama aikinsa na sabon shugaban kasar. Amma, bayan haka ba da dadewa ba, 'dan dakara daban, kuma tsohon firaministan kasar, Alassane Ouattara shi ma ya yi rantsuwar hawan kujerar mulkin kasar. A ranar 3 ga wata, kwamitin kula da tsarin mulki na kasar Kodivwa ya sanar da cewa, Laurent Gbagbo ya samu nasara bisa kuri'un da ya samu na kashi 51.45 cikin kashi 100, har ma ya soke sakamakon da kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar ya sanar a ranar 2 ga wata game da Alassane Ouattara ya samu nasara bisa kuri'un da ya samu na kashi 54.1 cikin kashi 100. (Bilkisu)