in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar yanayi ta kasar Sin ya bukata a tsaya kan manufar daukan nauyi iri daya amma tare da bambanci wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi
2010-12-04 18:15:03 cri
Zheng Guoguang, shugaban hukumar yanayi ta kasar Sin, ya furta a nan birnin Beijing na kasar Sin a ranar 2 ga wata cewa, manufar daukan nauyin iri daya amma tare da bambanci ta kasance tushe ga hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasashe daban daban don tinkarar matsalar sauyin yanayi.

A wajen wani dandalin tattaunawa dangane da yadda ake kokarin raya kimiyya da al'adu a kasar Sin da aka shirya a ran nan, Mista Zheng ya bayyana cewa, ya kamata a tabbatar da zaman daidaito a tsakanin kasashe daban daban yayin da suke tinkarar matsalar sauyin yanayi, hakan ya kasance hakkin da kasashe masu tasowa suka samu bisa yarjejeniyar tsarin tinkarar matsalar sauyin yanayi ta MDD.

Sa'an nan Zheng ya kara da cewa, akwai matalauta da marasa karfi da yawa a kasar Sin, haka kuma ya kasance wuraren da ke cikin kangin talauci da yawa a kasar. Shi ya sa aikin da kasar Sin za ta yi shi ne kokarin tabbatar da samun yanayi mai kyau wajen raya kasa, haka kuma bisa matsayinta na wata babbar kasa dake dauke da nauyi a wuya, za ta yi kokarin lallashin kasashen duniya da su tinkari matsalar sauyin yanayi tare. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China