in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gabatar da sakamakon farko na zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire
2010-12-03 16:39:49 cri

A ran 2 ga wata, shugaban hukumar zaben kasar Cote d'Ivoire mai zaman kanta ya sanar da cewa, dan takarar jam'iyyar adawa ta kasar Alassane Dramane Ouattara ya kada shugaban kasar na yanzu Laurent Gbagbo a zaben shugaban kasar zagaye na biyu. Saboda rashin bayyana sakamakon zaben cikin kwanaki 3 bayan gudanar zaben, an bukaci kwamitin tsarin mulkin kasar ya amince da sakamakon, sabo da haka ba a kammala takarar dake tsakanin Gbagbo da Ouattara ba.

Bisa kididdigar da hukumar zaben kasar zaman kanta ta gudanar, an ce, Ouattara ya samu kashi 54.1 cikin kashi dari na kuri'un da aka kada, yayin da Gbagbo ya samu kashi 45.9 cikin kashi dari, sabo da haka Ouattara ya yi nasara a zaben shugaban kasar zagaye na biyu. Jama'ar kasar sun watsa labarin bayan da aka gabatar da sakamakon, kana masu goyon bayan Ouattara sun fara yin murnar lashe zaben.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China