Duk da cewa akwai wasu tasoshin jefa kuri'un da ba su bude cikin lokaci ba, amma an gudanar da zaben shugaban kasar yadda ya kamata. An ce yawan mutane da suka jefa kuri'u a zagaye na biyu ya ragu sosai bisa na zagayen farko.
'Yan takaran biyu na zaben shugaban kasar a zagaye na biyu wato tsohon firaministan kasar Alassane Dramane Ouattara da shugaban kasar na yanzu Laurent Gbagbo sun jefa kuri'a a wata mazaba dake birnin Abidjan, babban birnin kasar. Bayan da suka jefa kuri'a, sun bayyana cewa, suna da imanin cin nasara. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar za ta bada sakamakon zaben a cikin kwanaki 3 masu zuwa.(Zainab)