in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kaddamar da wani aiki na taimakawa wadanda ke fama da ciwon yanar ido a kasar Zimbabwe
2010-11-24 16:11:11 cri
Ranar 23 ga wata da dare, a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, an kaddamar da wani aiki mai suna "ziyarar sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe", tare da nufin taimakawa jama'ar kasar Zimbabwe wadanda suke fama da matsalar yanar ido.

A nasa bangaren, shugaban tawagar masu ayyukan jinya ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban asibitin Tongren dake birnin Beijing Mista Han Demin ya ce, a cikin tsawon mako daya, kwararrun likitoci hudu a fannin idanu za su yi aikin tiyata ga mutanen kasar Zimbabwe 400, wadanda suke fama da ciwon yanar idanu. Mista Han ya bayyana cewa, wannan ne karon farko da aka shirya irin wannan aiki na taimakawa wadanda suke fama da matsalar idanu a nahiyar Afirka.

Har wa yau kuma, a madadin shugaba Robert Mugabe gami da jama'ar kasar Zimbabwe, ministan tsaron kasa na Zimbabawe Mista Emmerson Mnangagwa ya nuna maraba ga zuwan tawagar masu ayyukan jinya ta kasar Sin da hannu biyu-biyu, ya kuma bayyana cewa, wannan lamari ya sake shaida irin kyakkyawar dangantakar abokantaka dake tsakanin jama'ar kasashen Sin da Zimbabwe.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China