Ba da dadewa ba, Bambi ya hau dakinsa, ya fitar dukkan gindin kare. Bayan haka, Bambi ya yi tunani da cewa, "Ko ya fidda duka, yaya zai yi da su?" Amma bayan wata daya kawai, an sake samun gindin kare da yawa bisa rufin daki. Bambi ya yi farin ciki, ya kyautata zaton cewa, "Yanzu dai ina da gindin kare da yawa, kamata ya yi na raba wasu ga abokaina." Banbi ya ba dan biri 10, ya ba doki 11, kuma ya ba kare 9, sannan ya ba kyanwa 5, yayin da ya ba Panda 20. Abokan Bambi suka nuna farin ciki, dukkansu sun bayyana cewa, Bambi yana da kirki.
A kashegari, Bambi ya kai ziyara a lambun shan iska tare da abokinsa kare. Lambun shan iska na da kyan gani sosai, tare da furanni masu launuka iri-iri. An samu abubuwan wasanni daban daban, kamar jirgin sama, da jirgin kasa, da motar dake ratsa duwatsu da dai sauransu. Bambi ya yi wasa a wannan wuri tare da kare. Dukkansu sun yi farin ciki kwarai.
Ya zuwa lokacin rana, bayan da suka ci abinci, Bambi da kare sun kama hanyar gida. A kan hanyarsu, sun duba gajimare dake sauyawa a kullum, da babbar ganuwa mai ban girmamawa. Dukkansu sun farantar da zuciyar Bambi da abokinsa. Amma a kai a kai sun fahimci cewa, sun bace. Daga bisani, sun samu wata hanya. Bambi da kare sun bi wannan hanya sun ci gaba da tafiya a kai a kai. Amma ba da dadewa ba, Bambi ya bayyana cewa, "Kare, na gaji sosai. Bari mu tsaya mu kwana a wannan wuri!" Kare ya amsa cewa, "Madalla!" (Fatima)
A kashegari da safe, Bambi ya sake kama hanya tare da kare. Amma ba da dadewa ba, kare ya bayyana wa Bambi cewa, "Lokacin rana yayi, bari mu je mu ci abinci tukuna." Bambi ya ce, "Madalla!" A kai a kai, lokacin yamma ya yi. Bambi da kare sun kusan shiga daji. Yayin da suka ci karo da wata alamar hanyar, inda aka rubuta cewa, "Daji yana kan gaba!" Da ganin haka, Bambi da kare dukkansu sun yi farin ciki, su ci gaba da kama hanya. Amma a kai a kai lokacin dare ya yi. Bambi da kare ba su koma gida ba. Ina dalilin da ya sa haka? A daidai wannan lokaci, kare ya tarar da gidansa, ya ce, "Bambi, a hakika dai, mun riga mun zo gida!" Bambi ya amsa cewa, "Lallai! Mun zo gida!"