To, mun gode, mai sauraronmu a kullum malam Nuraddeen Ibrahim Adam. Mu ma muna farin ciki sosai da wannan labari. Kamfanonin kasar Sin suna kokari sosai wajen tabbatar da ingancin kayayyakin da suke samar. Muna fatan wadannan kamfutoci da kasar Sin za ta samar za su ba da taimako a cikin babban zaben kasar Nijeriya a shekarar 2011 yadda ya kamata. Da fatan za a gudanar da zaben lami lafiya.
Sakon malam Nuraddeen Ibrahim Adam ke nan. Bayan haka, malam Bello Gero a Sokoto, tarayyar Nijeriya ya bayyana mana cewa, "Ina mai matukar nuna farin cikina zuwa ga dukkanin ma'aikatan sashen hausa na CRI don gane da kulawarku a gare ni da kuma iyalina. Ina mai sanar da ku cewa, yarinyar da aka haifar mini tana nan lafiya lau, kuma an rada mata suna Halimatu Sadiya. Tana nan cikin koshin lafiya tare da mahaifiyarta da kuma sauran iyali baki daya. Bayan haka, nan ba da dadewa ba, za ku sami hotonta idan Allah ya so ya yarda."
To, malam Bello Gero, muna taya maka murna sosai da sosai. Kuma muna fatan ganin hoton diyarka cikin sauri, ko shakka babu, za ta yi kyan gani kwarai da gaske. Da fatan za ta girma lami lafiya, tare da farin ciki.
Sakon malam Bello Gero ke nan. A makon jiya, malam Adamu Issa a Kano, tarayyar Nijeriya ya yi mana tambayar cewa, "Don Allah ko za ku ba da wani bayani dangane da Norman Bethune?" To, malam Adamu Issa, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya, da fatan kana sauraronmu.
An haifi Norman Bethune a shekarar 1890 a garin Gravenhurst na jihar Ontario ta kasar Canada. Ya kammala karatunsa a kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Toronto a shekarar 1916. Daga bisani, an zabe shi a matsayin memba na majalisar likitancin kirji a shekarar 1935. Ya yi suna sosai a sashen likitanci na kasar Canada, Birtaniya da Amurka. A watan Nuwamba na wannan shekara, ya shiga jam'iyyar kwaminis ta kasar Canada.
Bayan abkuwar yakin Spainiya a shekarar 1936, ya jagoranci wani rukunin likitoci zuwa Madrid domin ba da jiyya ga jaruman sojoji masu yaki da Fasist. A shekarar 1937, yaki da hare-haren sojojin Japan a Sin ya barke. Bethune dake samar da kudi ga yakin Spainiya a Canada da Amurka ya yi jawabi cewa, "Ana hakikanin yaki a kasar Sin, wanda zai tabbatar da makomarmu baki daya. Dole ne na yi gwagwarmaya tare da su!"
A watan Janairu na shekarar 1938, bisa umurnin jam'iyyar kwaminis ta kasar Canada da ta Amurka, Bethune ya jagoranci wani rukunin likitocin Canada da na Amurka tare da na'urori da dama zuwa kasar Sin, domin ba da taimako ga jama'ar kasar. Bayan shan wahalhalu da yawa, a karshen watan Maris na shekarar 1938, Bethune ya isa Yan'an, inda Mao Zedong ya yi maraba da zuwansa, tare da nuna babban yabo ga ziyararsa a Sin domin ba da agaji. Daga bisani Bethune ya je fagen yaki nan take. A cikin shekaru 2 a lokacin, Bethune ya yi aiki matuka tare da sadaukar da kansa domin ba da jiyya ga sojojin JKS.
A kokarin kyautata yanayin kiwon lafiya a yankin yaki da sojojin Japan, Bethune ya ba da shawarar kafa kamfanin samar da kayayyakin kiwon lafiya, a kokarin daidaita matsalar karancin magunguna. Kuma ya ba da kos na koyar da ilmin likitanci, tare da kafa dakuna da rumfunan ba da jiyya 13 ga rundunar sojan Jizhong. A watan Yuni na shekarar 1939, bayan da ya koma yankin Jixi, Bethune ya kafa makarantar kiwon lafiya, ya tabbatar da kos da kansa, tare da rubuta littattafai kimanin 20. Ya yi aiki matuka. A cikin wasikar da ya aika wa abokinsa na Canada, ya rubuto cewa, "Lallai ina gajiya sosai. Amma ina farin ciki kwarai, sabo da ana bukatar taimako da nake bayar sosai."
A karshen watan Oktoba na shekarar 1939, yayin da yake ba da jiyya ga sojoji da suka ji rauni a gundumar Laiyuan ta lardin Hebei, daya daga cikin yatsunsa na hannun hagu ya raunata. Amma bai ta da hankali ko kadan ba. Ya ci gaba da aikinsa har tsawon rayuwarsa. A ran 12 ga watan Nuwamba na shekarar 1939, Bethune mai shekaru 49 da haihuwa ya rasu a kauyen Huangshikou dake gundumar Tang ta lardin Hebei na Sin.
A ran daya ga watan Disamba na wannan shekara, sassa daban daban na Yan'an sun gudanar da bukukuwan tunawa da likita Norman Bethune.
A watan Disamba na shekarar 2009, a cikin wani aikin da gidan rediyon kasar Sin da hukumar sada zumunci a ketare ta jama'ar kasar Sin, da hukumar kula da kwararrun ketare ta kasar suka shirya, Norman Bethune ya zama daya daga cikin abokanmu na kasashen waje guda 10 da suka fi sada zumunci a kasar Sin.(Fatima)