Sanusi: Ko da yake yanzu ba a ambaton hanyoyin mota na yankunna karkara ba, amma gaskiyar magana ita ce a cikin shekaru da yawa da suka wuce, an samu ci gaba sosai wajen shimfida hanyoyin mota a yankunan karkara. A gun wani taro mai nasaba da batun hanyoyin mota na yankunan karkara, da aka yi a lardin Shandong a kwanan baya, Mr. Feng Zhenglin, mataimakin ministan ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin ya bayyana wa mahalarta taron fiye da dari 4 halin da ake ciki, cewar "Gwamnatin kasar Sin na mai da hankali sosai kan aikin gina hanyoyin mota a yankunan karkara. Bisa kokarin da ta yi cikin shekaru da yawa da suka gabata, hanyoyin mota da aka gina a yankunan karkara sun samu kyautatuwa. An yi hasashen cewa, ya zuwa karshen bana, tsawonsu zai kai kilomita miliyan 3 da dubu 450. Haka kuma, hanyoyin mota na yankunan karkara sun taka muhimmiyar rawa wajen zamanintar da yankunan karkara da kara yawan kudin shiga da manoma suke samu. Sakamakon haka, sun kasance wata muhimmiyar kafa dake zamintar da yankunan karkara na kasar Sin."
Ibrahim: Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2009, tsawon hanyoyin mota da aka gina a yankunan karkara na kasar Sin ya kai fiye da kilomita miliyan 3 da dubu dari 3 wadanda suke hade da kusan dukkan kananan garuruwan dake yankunan karkara. Amma a shekarar 1978, jimillar tsawonsu kimanin kilomita dubu 586 ne kawai, kuma babu hanyar mota ko da kilomita daya a yawancin kananan garuruwan dake yankunan karkara.
Sanusi: Ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin gina hanyoyin mota a yankunan karkara ya jawo hankalin gamayyar kasa da kasa sosai. Sabili da haka, kawancen kungiyoyin kula da hanyoyin mota ta kasa da kasa ta bai wa ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin lambar yabo ta samar da "hanyoyin mota na yankunan karkara da adalcin dake kasancewa a zaman al'umma" domin yabawa kasar Sin sabo da kyakkyawan sakamako da ta samu wajen gina hanyoyin mota a yankunan karkara. Mr. Kapila, shugaban wannan kawance ya kuma yaba wa kokarin da kasar Sin ta yi wajen gina hanyoyin mota a yankunan karkara, inda ya ce, "Kasar Sin ta samu kyakkyawan sakamako sosai wajen gina hanyoyin mota, musamman a yankunan karkara. Ina fatan za ta ci gaba da yin haka a nan gaba."
Ibrahim: Shi kuma, Mr. Kabila yana ganin cewa, hanyoyin mota da aka gina a yankunan karkara sun taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar talauci a kasar Sin. Yana fatan sauran kasashe masu tasowa su yi koyi da kasar Sin wajen gina hanyoyin mota a yankunan karkara domin kyautata rayuwar manoma.
Sanusi: Ko da yake kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen gina hanyoyin mota a yankunan karkara, amma kuma tana fuskantar kalubale sosai, sabo da ba a samu daidaito a tsakanin yankuna daban daban wajen neman ci gaba, kuma jama'a ba su san yadda za su iya kare hanyoyin mota daga lalacewa ba, har ma ba a san yadda za a iya kulawa da hanyoyin mota dake yankunan karkara ba. Game da wadannan kalubale, Mr. Niu Jiatang, shugaban hukumar zirga-zirga ta birnin Zaozhuang ya ce, "Kulawa da hanyoyin mota dake yankunan karkara hakki ne na jama'a. Lokacin da yawancin jama'a ba su san yadda za su kiyaye su ba, dole ne gwamnati ta ba da jagoranci. Sabo da haka, gwamnatin lardin Shandong ta kebe wasu kudi domin kiyaye ingancin hanyoyin mota na yankunan karkara musamman." (Sanusi Chen)