in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aikin taimakawa 'yan Afirka kimanin dubu 1 wajen warware matsalolin da suka shafi idanu
2010-11-19 14:49:00 cri

A ran 18 ga wata a nan birnin Beijing, aka fara aikin taimakawa 'yan Afirka kimanin dubu 1 wajen warware matsalolin da suka shafi idanu.

Kungiyoyi masu zaman kansu da kamfanoni tare da wasu sassan ba da jinya na kasar Sin masu yawa sun gudanar da wannan aiki, za a tura rukunin ba da jinya dake kunshe da mutane fiye da 20 zuwa kasashen Malawi da Zimbabwe. A cikin mako daya mai zuwa, za a ba da jinya ga masu fama da matsalar ido kimanin dubu daya a kasashen biyu ba tare da biyan kudi ba.

Jakadun kasasahen biyu dake kasar Sin da wakilin hukumar kiwon lafiya ta MDD da sauran mutane da yawansu ya kai kimanin dari daya sun halarci bikin kaddamar da wannan aiki. Jami'an ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen Malawi da Zimbabwe sun bayyana a gun bikin cewa, wannan aiki zai inganta sha'anin kiwon lafiya a nahiyar Afirka, da kuma zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China