Mista Wen Gang ya ce, a kasashen Afirka da dama, ana iya ganin gadoji da hanyoyin da kasar Sin ta gina, kuma ma'aikata Sinawa suna nuna kwazo wajen gina muhimman ayyukan biyan bukatun jama'a a kasashen Afirka, ciki kuwa har da shimfida hanyoyi, gina gadoji da sauransu. Ya zuwa yanzu, ma'aikatan kasar Sin sun shafe tsawon shekaru sama da 50 suna kokarin bada taimako wajen gina gadoji da hanyoyi a nahiyar Afirka. Mista Wen ya kuma waiwayi wahalhalun da Sinawa suka fuskanta yayin da suke kokarin raya sana'o'insu a kasashen Afirka, da bayyana yadda kamfanonin kasar Sin suka samu bunkasuwa a wurin, gami da manyan sauye-sauyen da nahiyar Afirka ta samu a sabon halin da ake ciki.
Mista Wen Gang ya ce, yana fatan gadoji da hanyoyin da kasar Sin ta gina a kasashen Afirka za su kasance tamkar wata babbar gada dake sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a kokarin bayar da gudummawa ga mu'amala da ci gabansu.(Murtala)