in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kamfanin Touchroad mai sarrafa hada-hadar kudi na duniya ya yi magana da wakilinmu na CRI
2010-11-11 15:29:49 cri
Aikin ba da "Lambar yabo ta ba da gudummawa ga sada zumunci tsakanin Sin da kasashen Afirka-Kamfanonin Sin guda 10 da suka fi karbuwa a kasashen Afirka" ya riga ya shiga zagayen zaben kamfanoni 10 daga cikin 20, wanda hukumar sada zumunci tsakanin jama'ar Sin da ta kasashen Afirka, da gidan rediyon kasar Sin CRI suka shirya tare da kamfanin buga mujalla mai suna Afirka. A matsayin daya daga cikin kamfanoni dake takara, shugaban kamfanin Touchroad mai sarrafa hada-hadar kudi na duniya He Liehui ya yi magana da wakilinmu na CRI.

A yayin da yake magana, He Liehui ya waiwayo matsalolin da ya gamu da su a lokacin da ya fara aiki a nahiyar Afirka. Yanzu kamfaninsa ya riga ya bunkasa daga wani kamfanin saka zuwa wani babban kamfani dake da hanyoyi a fannoni daban daban, kamar bunkasa yankin masana'antu, da haka ma'adinan kasa, da kafa kamfanoni, da yin cinikayya da ketare, da yi musayar al'adu, da bunkasa sha'anin yawon shakatawa da dai sauransu.

A cikin shekarun da suka gabata, akwai dankon zumunci a tsakanin kamfanin Touchroad da kasashen Afirka. A sabili da haka, kamfanin ya ba da gudummawa sosai wajen bunkasa nahiyar Afirka, tare da samun kyakkyawar moriyar tattalin arziki da ta zamantakewar al'umma. A ganin He Liehui, kamata ya yi kasashen duniya su kara samun fahimtar Afirka, tare da kara mai da hankali wajen zuba jari a nahiyar. Abubuwan da nahiyar Afirka ke bukata, ba ma kawai bunkasa cinikayya ba, har ma bunkasa sana'ar kere-kere ta wurin, da bunkasa masana'antun zamani da tattalin arziki daga fannoni daban daban. Kamata ya yi a kara amfani da albarkatun nahiyar Afirka a fannin samun ci gaban tattalin arzikin nahiyar da kawo wa jama'ar kasashen Afirka alheri. Kamfanin Touchroad ya canza hanyar da yake bi daga bunkasa cinikayya a farko zuwa kafa kamfanin saka a Afirka, a kokarin canza hanyar samar da kayayyaki daga kasar Sin zuwa kasashen Afirka. Dadin dadawa, ma'aikatan kamfanin sama da kashi 98 cikin kashi dari 'yan asalin Afirka ne. A sabili da haka, an samar da guraben aikin yi da dama ga mazaunan wurin. A sa'i daya, kamfanin ya kafa wani yankin masana'antu a Botswana, a kokarin jawo hankalin mafi yawan kamfanoni wajen zuba jari a kasar, tare da samar da guraben aikin yi, da sa kaimi ga musayar fasahohi. Bayan haka, kamfanin Touchroad ya ba da kulawa sosai ga wadanda suke fama da talauci, da fatan zai ba da taimako a gare su baki daya.

Makasudin gudanar da wannan zabe, shi ne tabbatar da gudummawar da kamfanonin kasar Sin suke bayar a yunkurin bunkasa nahiyar Afirka, tare da bayyana dankon zumunci dake tsakanin jama'ar Sin da ta nahiyar Afirka a sabon zamani.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China